News
Jami’an Hukumar NAFDAC Sun Gano Lita 88,000 Na Sinadaran Haɗa Abubuwan Fashewa A Kano
Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta gano tare da rufe wani ɗakin ajiya da ke cike da sinadarai masu matuƙar haɗari a unguwar Kwakwachi da ke ƙaramar hukumar Fagge, Jihar Kano.
Darakta-Janar na hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta bayyana hakan a lokacin da take zantawa da manema labarai a wurin a ranar Laraba, inda ta ce sinadarai da ake amfani da su wajen ƙera abubuwan fashewa ne aka gano a cikin ɗakin.
EFCC Ta Cafke Daliban BUK 24 Da Ake Zargi Da Damfara Ta Yanar Gizo A Kano
Farfesa Adeyeye, wacce ta samu wakilcin Daraktan Bincike da Aiwatarwa na hukumar, Dr. Martins Iluyomade, ta ce an gano sinadarai biyu masu haɗari a wurin, da suka haɗa da lita 60,000 na sulphuric acid mai ƙarfi 90.5%, da kuma lita 28,560 na nitric acid mai ƙarfi 68%.
Haka kuma, an gano jarkoki 330 da aka riga aka fitar da abin da ke cikinsu, inda ba a san inda aka kai su ko mutanen da suka karɓa ba.
A cewar Farfesa Adeyeye, jami’an NAFDAC ne suka gano wannan wuri yayin da suke gudanar da aiki na musamman, inda suka kama manajan ɗakin ajiyar, wanda shi kaɗai ne aka samu a wurin a lokacin.
Ta ce bincike na ci gaba don gano wanda ya mallaki ɗakin da kuma ƙarin bayani dangane da batun.
Farfesa Adeyeye ta tabbatar wa da al’umma cewa hukumar za ta lalata sinadaran nan da ta kama cikin tsari daidai da ƙa’idojin NAFDAC domin kare lafiyar jama’a da kuma tabbatar da tsaron ƙasa.
“Mun ɗauki matakin da ya dace, kuma za mu cigaba da bin diddigi domin gano masu hannu a cikin wannan aiki mai hatsari,” in ji ta.
