News
Hatsarin Mota Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 12 Tare Da Jikkata 5 A Kano
Hatsarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 12 tare da jikkatar wasu biyar a safiyar Juma’a, a kauyen Samawa, cikin karamar hukumar Garun Malam, jihar Kano.
Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) reshen Kano ta ce hatsarin ya faru ne misalin ƙarfe 2:40 na asuba a kan babban titin Zariya–Kano.
Kotun Canada Ta Ayyana Jam’iyyun PDP Da APC A Matsayin Ƙungiyoyin Ta’addanci
Kakakin FRSC a jihar, ya bayyana cewa lamarin ya shafi babbar motar tirela ta DAF CF95 wadda ke ɗauke da kaya da kuma fasinjoji.
“Mutum 12 daga cikin 19 da ke cikin motar sun mutu nan take, biyar sun jikkata, yayin da biyu suka tsira ba tare da wata matsala ba,” in ji FRSC.
An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Kura, yayin da aka ajiye gawarwakin mamatan a Asibitin Nassarawa.
