News
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Uku, Sun Yi Garkuwa Da Wasu A Kano
Akalla mutane uku sun rasa rayukansu, yayin da wasu uku suka fada hannun ‘yan bindiga a wani sabon hari da aka kai a kananan hukumomin Shanono da Tsanyawa a Jihar Kano.
Majiyoyi daga yankin sun ce, ‘yan bindigar dauke da makamai masu yawa sun shigo jihar ta iyakar Katsina, inda suka fara kai hari a garuruwan Yanganau da Tsanyawa tun yammacin ranar Alhamis.
Trump Ya Yi Barazanar Turo Sojojin Amurka Su Mamaye Nigeria Kan Zargin Kisan Kiristoci
Bincike ya nuna cewa, jami’an tsaro sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar, inda suka fatattaki su daga wurin harin farko. Babu wanda aka ji rauni, sai dai an sace wasu dabbobi.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa, “Sun fito ne daga Kogari, Musawa/Matazu, Jihar Katsina. Jami’an tsaro sun samu labari misalin karfe 5:30 na yamma, amma bayan musayar wuta, ‘yan bindigar suka tsere.”
Sai dai, bayan sun ci tura a Tsanyawa, ‘yan bindigar suka ci gaba da kai hare-hare a Yar Tsamiya, Faruruwa da Shanono misalin karfe 1:30 na dare.
A nan ne suka kashe mutane uku sannan suka yi garkuwa da wasu uku kafin su tsere.
Farfesa Muhammad Dauda daga Kuraku ya ce, “A cikin kwanaki uku, hare-hare sun shafi unguwanni Tsamiya, Yaudari da Yanganau. Mutane sun mutu, wasu kuma sun bace. Mutanenmu suna kwana a daji ko wurin ‘yan uwa saboda tsoro.”
Har zuwa yanzu, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa ta hukuma ba.
