Politics
Kungiyar Matasan APC Ta Nemi Ayi Budadden Bincike Kan Kudaden Kamfen Din Gawuna
Wata ƙungiyar matasan jam’iyyar APC mai suna Coalition of APC Progressive Youths Group ta nemi uwar jam’iyyar a matakin ƙasa ta gudanar da bincike kan yadda aka tara da kuma yadda aka kashe kudaden kamfen zaɓen gwamnan Kano na 2023.
A cikin takardar da ƙungiyar ta aika wa shugaban jam’iyyar APC a Abuja, wacce aka sanya wa hannu ranar 7 ga Nuwamba 2025, matasan sun ce akwai tambayoyi masu yawa game da gaskiya da sahihancin wasu daga cikin kudaden da aka karɓa a lokacin kamfen na Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ɗan takarar jam’iyyar a wancan lokacin.
An Garzaya Da Daruruwan Mutane Zuwa Asibiti Sakamakon Fashewar Bam A Masallacin Juma’a
Shugaban ƙungiyar, Comrade Sadiq Ali Sango, ya rubuta cewa binciken zai taimaka wajen tabbatar da bin doka — ciki har da ka’idojin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da kuma dokokin kudi na cikin jam’iyya.
Takardar ta nemi jam’iyyar APC ta bayyana takardun jerin sunayen masu bada gudummawa da yadda aka kashe kudaden.
Da kuma ba da damar duba bayanan banki da sauran mu’amalar kudi da suka shafi kamfen ɗin.
Sai Tattauna da jami’an kamfen da suka shugabanci tara kudaden.
Sai kuma Fitar da rahoton bincike cikin kwanaki bakwai bayan fara aikin.
Ƙungiyar ta ce wannan mataki zai inganta gaskiya da amincewa a cikin jam’iyya, musamman a cikin manyan shirye-shiryen siyasa.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
