News
Matar Da Ta Shirya Kashe Mijinta Kan Naira Dubu 400 Ta Faɗa Komar ’Yan Sanda A Kaduna
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna ta cafke wata mata mai suna Nafisa Salisu, bayan zargin cewa ta ɗauki hayar wasu matasa su kashe mijinta,Sani Abubakar, a unguwar Rafin Guza da ke Kaduna ta Arewa.
Kakakin rundunar, SP Mansur Hassan, ya shaida cewa an kama matasan da ake zargi da shiga lamarin, kuma sun haɗa da Isma’il Alhassan (Dogo), Sulaiman Ibrahim, da kuma Monday Magaji.
Kano: Gwamnati ta fara aikin sanya fitilun Kan Hanya A Dangoro
A cewar rundunar, jarin kasuwancin da mijin ya bai wa matarsa — kimanin Naira dubu 400 — ya salwanta. Hakan ne ya sa ta nemi wadanda za su kashe shi, inda ta amince za ta biya su Naira dubu 80.
Nafisa ta fara biyan su Naira dubu 50, sannan ta ƙara ba su Naira dubu 5 domin su siyo maganin bacci da za su yi amfani da shi kafin su kai wa mijin hari. Bayan kammala aikin kuma ta yi alƙawarin cika sauran kuɗin da suka kai Naira dubu 30.
Sai dai duk da harin da suka kai masa da wuka, mijin bai mutu ba, inda aka garzaya da shi asibiti. Rundunar ta ce an kama dukkan waɗanda ake zargi, kuma bincike na ci gaba kafin a gurfanar da su gaban kotu.
