Sports
Makomar Werner, Antony, Pogba, Nunez, Eriksen, Bellingham
Daga Muhammad Muhammad zahradd
Dan kwallon Jamus da ke murza leda a Chelsea, Timo Werner, yana son barin kungiyar kuma the Blues sun ce ba za su hana shi tafiya ba idan dai aka biya kudin da suka sanya a kansa wanya ya kai yuro 40m. (Sport1)
Idan Erik ten Hag ya zama kocin Manchester United, yana son dauko dan wasan Brazil Antony, mai shekara 22, daga kungiyarsa ta yanzu Ajax. (Telegraph)
Dole ne dan wasan tsakiyar Manchester United da Faransa Paul Pogba, mai shekara 29, ya aminci a zaftare albashi da alawus-alawus dinsa idan yana so ya komaJuventus a bazarar nan. (Calciomercato – via Mail)
Dan wasan gaban Benfica Darwin Nunez, mai shekara 22, wanda Tottenham ke zawarcinsa, zai tashi ne idan duk kungiyar da ke son sa za ta iya biyan Yuro miliyan 80 a bazara. (O Jogo – via Sport Witness)
Arsenal ta gabatar da tayin sayen dan wasan Feyenoord da Colombia Luis Sinisterra, mai shekara 22. (Corriere dello Sport).
Real Madrid ta bayyana dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jude Bellingham a matsayin wanda take zawarcinsa, duk da alaka mai karfi tsakanin dan wasan mai shekaru 18 da komawa Liverpool. (Bild)
Brentford na son tsawaita kwantiragin dan wasan tsakiya na Denmark Christian Eriksen, mai shekara 30 (Times)
Dan wasan bayan Manchester United dan kasar Ingila, Brandon Williams, mai shekara 21 wanda a halin yanzu yake zaman aro a Norwich, ya ce “babu wani amfani” idan ya koma Old Trafford domin ya sake neman gurbinsa. (Mails)
Har yanzu Barcelona ba ta yi tayin sayen dan wasan gaban Leeds Raphinha ba, amma an tattauna batun cikin sirri da wakilin dan wasan mai shekaru 25 (Fabrizio Romano)
Barcelona na fatan dan wasan Spain Adama Traore da ke zaman aro a kungiyar daga Wolves zai zama cikakken dan wasanta (RAC 1 Goal)
Atletico Madrid na iya tsawaita zaman aro na dan wasan gaban Faransa Antoine Griezmann mai shekaru 31 daga Barcelona amma ba su shirya barin dan wasan Portugal Joao Felix, mai shekara 22, ya koma kungiyar ta Sipaniya ba. (Goal)
Liverpool da Chelsea na zawarcin dan wasan Paris St-Germain dan kasar Faransa Ismael Gharbi mai shekaru 17. (Goal)
Arsenal ta shirya tsaf don barin dan wasan tsakiyar Uruguay Lucas Torreira, mai shekara 26 wanda a halin yanzu yake zaman aro a Fiorentina ya tafi dindindin a bazara, yayin da dan wasan Masar mai shekara 29, Mohamed Elneny shi ma zai tafi. (Fabrizio Romano)
Liverpool da Real Madrid na tunanin zawarcin dan wasan Porto dan kasar Portugal Vitinha mai shekaru 22. (Defensa Central)
Fiorentina na zawarcin dan wasan bayan Manchester United da Portugal Diogo Dalot, mai shekara 23. (Firenze Viola)
