News
Khamenei Ya Yi Gargaɗi Kan Yaƙin Yanki Idan Amurka Ta Kai Hari Kan Iran
Jagoran addini na Iran, Ali Khamenei, ya yi gargaɗin cewa duk wani farmakin da Amurka ta kai kan Iran zai iya haifar da yaƙin yanki.
‘Idan Amurka ta ƙaddamar da yaki a wannan karon, zai bazu zuwa ko’ina cikin yankin [Gabas ta Tsakiya],’ in ji Khamenei a wata ganawa a Tehran a ranar Lahadi, a gabanin bikin cikar shekaru 47 na Juyin Juya Halin 1979 wanda ya kawo karshen mulkin Pahlavi.
Jami’an Yan Sanda Sun Kama Mutane 21 Da Ake Zargin Da Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba A Zamfara
Ya yi watsi da tura jiragen ruwan soja na Amurka zuwa Tekun Fasha, yana mai cewa irin waɗannan matakai ‘ba sabon abu bane’.
Khamenei ya ce jami’an Amurka sau da yawa sun fito da irin waɗannan gargadi a baya, suna ikirarin cewa “Kowane zaɓi na kan tebur’, ciki har da amfani da karfin soja.
“Yanzu wannan mutumin ma kullum yana ikirarin cewa ‘mun kawo jiragen yaki’ da sauransu,” in ji Khamenei, yana nufin Shugaban Amurka Donald Trump.
“Kasar Iran kada ta firgita da irin waɗannan abubuwa. Mutanen Iran ba sa jin tasirin irin waɗannan barazanar,” in ji shi.
Iran ta ce duk maƙociyar da ta bari aka yi amfani da ita wurin kai mata hari ‘abokiyar gaba’ ce
A ranar Laraba, Trump ya rubuta a kafar sada zumunta cewa wani ƙaton jirgin ruwa mai dakon ɗaukar jiragen sama na kan hanyar zuwa Iran, yayin da ya yi kira ga Tehran da ta shiga tattaunawa nan take.
Wannan bayani ya haifar da zato game da yiwuwar farmakin soja na Amurka, ya kuma jawo martani mai ƙarfi daga jami’an Iran tare da hanzarin fara harkokin diflomasiyya a yankin.
“Kamar juyin mulki”
Khamenei ya jaddada cewa Iran ba za ta zama wadda ta fara kowane yaƙi ba kuma “ba ta neman kai hari ga kowace ƙasa.” Ya gargadi cewa za ta “mayar da martani mai ƙarfi ga duk wanda ya kai mata hari ko ya cutar da ita.”
Yayin da yake magana kan zanga-zangar adawa da gwamnati da suka faru kwanan nan, Khamenei ya bayyana su a matsayin kamar “juyin mulki’ wanda aka dakile a ƙarshe. Ya ce tashin hankalin ya nufi “halaka cibiyoyi masu muhimmanci da tasiri wajen tafiyar da ƙasa.”
Hukumomin Iran sun zargi Amurka da Isra’ila da tallafa wa abin da suka kira “masu tayar da tarzoma” da ‘’yan ta’adda’ waɗanda suka aikata tashin hankali yayin zanga-zangar.
