News
Little Ya Jajantawa Yan Kasuwar Singa Bisa Ibtila’in Gobara
Jigo a jam’iyyar ADC, Alhaji Ibrahim Ali Amin wanda aka fi sani da “Little,” ya mika sakon jajantawa ga ‘yan kasuwar Kasuwar Singer bayan gobarar da ta lalata kasuwar tare da haddasa asarar rayuka da dukiyoyi masu dimbin yawa.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook , ya bukaci Gwamnatin Jihar Kano da ta gaggauta tallafa wa wadanda gobarar ta shafa, yana mai cewa biyan diyya cikin kankanin lokaci zai taimaka wajen rage radadin asarar da suka yi.
Gobara Ta Lalata Shaguna Sama Da 1,500 A Kasuwar Singer Dake Kano
Ya kuma yi kira ga gwamnatocin jiha da ta tarayya da su samar da kayan aikin kashe gobara na zamani ga Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, domin hana sake aukuwar irin wannan iftila’i a nan gaba.
Haka kuma ya yaba wa kamfanoni masu zaman kansu da suka kawo motocin kashe gobara domin taimakawa wajen dakile gobarar, yana mai cewa taimakon nasu ya taka muhimmiyar rawa wajen rage girman barnar.
Little ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa wadanda suka rasu, tare da mayar wa wadanda suka yi asara abin da suka rasa.
