Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Wa’adin Shekaru Shida Kafin Kafa Sabbin Manyan Makarantu A Najeriya

Published

on

images (6)
Ministan Ilimi Olatunji Alausa,
Advertisements
ads

Gwamnatin tarayya ta sanya wa’adin shekaru shida kafin kafa manyan makarantu a fadin kasar nan.

Da yake yiwa manema labarai jawabi bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya a ranar Laraba a Abuja, Ministan Ilimi Olatunji Alausa, ya ce an dauki matakin ne domin inganta harkar ilimi a fadin kasar.

Peter Obi Ya Danganta Talaucin Najeriya Da Rashin Nagartaccen Shugabanci

Da yake bayyana ci gaban, Ministan ya ce tun da fari an dakatar da kafa jami’o’i masu zaman kansu a shekarar da ta gabata.

Ya kara da cewa a yanzu sabon umarnin ya shafi dukkan manyan makarantu da su ka hada da jami’o’i da kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi.

Ya ce a Najeriya akwai manyan makarantu, na gwamnati da masu zaman kansu, a don haka su na buƙatar taimakawa cibiyoyi masu zaman kansu su kasance masu dorewa musamman a fannin kuɗi.

Advertisement

Ya ce kimanin ‘yan Najeriya miliyan 2.3 ne suka nemi rubuta jarabawar JAMB a shekarar da ta gabata, amma duk da haka kusan jami’o’i 228 ne su ka samu kasa da 50 da su ka nemi shiga.

Ya kara da cewa, idan aka warware matsalolin da suka shafi kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU, akwai yuwuwar karin dalibai su shiga jami’o’in gwamnati, wanda hakan na iya kara rage daukar nauyin makarantu masu zaman kansu.

Ya jaddada bukatar kare jarin da masu zaman kansu ke yi tare da inganta inganci a makarantun gwamnati da masu zaman kansu

Ministan ya kuma bayyana cewa, ma’aikatar da majalisar sun amince da mayar da hukumar kula da ilimin manya ta kasa, wadda a baya aka mayar da ita wani sashe a cikin ma’aikatar.

Ya bayyana cewa matakin ya yi daidai da shirin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na samar wa da sama da ‘yan Najeriya miliyan 50 ilimin zamani a cikin shekaru biyu zuwa uku masu zuwa.

Alausa ya bayyana cewa, kasancewar kimanin ‘yan Najeriya miliyan 56 da har yanzu ba su iya karatu ba, da mayar da hukumar zuwa matsayinta na baya, zai karfafa kokarin da ake na bunkasa ilimin manya na karatub boko, musamman a yankunan karkara ta hanyar rediyo da talabijin da fadakarwa da kuma cibiyoyin koyo..

Advertisement

 

 

Vanguard

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending