News
Gwamnatin Lagos Ta Kama Mutane 275 Saboda Yin Bahaya A Waje
Gwamnatin Jihar Lagos ta kama mutane 275 a sassa daban-daban na jihar saboda yin bahaya a waje, duk da cewa akwai bandakunan jama’a da Gwamnatin ta gida guda 8,710 da ke aiki.
Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Ruwa, Tokunbo Wahab, ya ce an yi waɗannan kamun tun daga ranar 1 ga Janairu. Ya bayyana cewa mutane kusan 70 ne aka kama a Tsibirin Lagos, 62 a Berger, yayin da wasu 43 aka kama a Oshodi suna yin bahaya a waje.
Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Wa’adin Shekaru Shida Kafin Kafa Sabbin Manyan Makarantu A Najeriya
“Yin bahaya a waje laifi ne. Muna da bandakuna masu aiki a duk fadin jihar, ciki har da gidajen abinci da tashoshin mota,” in ji Wahab.
Ya ƙara da cewa akwai ƙungiyar yaki da yin bahaya a waje wacce ke yawo kowace rana, musamman karfe 3, 6, da 7 na safe, don hana wannan dabi’a. “Muna kama masu laifi mu kai su kotu a kullum.
A shekarar 2024, Hukumar Kula da Muhalli ta Jihar Lagos tare da ta Jihar Ogun sun kaddamar da shiri domin kawo ƙarshen yin bahaya a waje a kan hanyar Lagos–Ibadan Expressway.
Wannan na nufin kare lafiya da tsaftar muhalli, da rage yaduwar cututtuka kamar sankarau.
Rahoton UNICEF na 2022 ya nuna cewa rashin tsafta na kashe yara sama da 100,000 a Najeriya duk shekara, musamman saboda gudawa da rashin ruwa mai tsafta.
