News
An Kashe Ministan Tsaron Mali A Harin Ta’addanci
Rahotanni daga Al Jazeera sun bayyana cewa an kashe Ministan Tsaron ƙasar Mali, Sadio Camara, a wani hari da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kai a ranar Lahadi.
Majiyoyin labarai sun ce maharan sun kai farmaki gidan ministan da ke garin Kato, wanda ke kimanin kilomita 15 arewacin Bamako, babban birnin ƙasar.
An Kashe Ministan Tsaron Mali A Harin ‘Yan Ta’adda
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a fitar da cikakken bayani kan yadda harin ya faru ba, yayin da hukumomin tsaro ba su yi cikakken bayani kan lamarin ba. Sai dai wannan harin na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar Mali ke fuskantar ƙalubalen tsaro daga kungiyoyin ‘yan ta’adda a sassa daban-daban na ƙasar.
Ana sa ran gwamnati za ta fitar da ƙarin bayani kan wannan lamari a nan gaba, yayin da jama’a ke ci gaba da nuna damuwa kan yadda hare-haren ta’addanci ke ƙaruwa a ƙasar.
