Connect with us

News

Kwantena Ta Murkushe Wata Motar Haya

Published

on

1000186786

Wata Tirela ɗauke da kwantena mai ƙafa 40 ta haddasa mummunan hatsari a yankin Second Rainbow da ke hanyar Oshodi a jihar Legas, inda ta kife kan wata motar haya tare da jikkata wata mata mai sana’ar POS.

Hukumar Kula da Zirga-zirga ta Jihar Legas (LASTMA) ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne a gefen titin da ke kusa da ofishin Ƴansanda  Tactical Team, bayan motar ta kasa daidaita tafiyarta yayin da take kan hanya.

Advertisement

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Matashi Kan Yaɗa Bidiyon Harin Ƴan Bindiga Na Ƙarya A TikTok

Rahotanni sun nuna cewa motar ta kauce daga hanyar da take bi kafin daga bisani ta kife kan wata motar haya tare da afkawa wasu shaguna da ke bakin titi, lamarin da ya haddasa babbar barna.

Advertisement

Matar da ke gudanar da sana’ar POS a ƙarƙashin wata rumfa kusa da wurin hatsarin ta samu munanan raunuka a ƙafafunta biyu.

Jami’an LASTMA sun isa wurin cikin gaggawa domin shawo kan cunkoson ababen hawa tare da haɗa kai da sauran jami’an agajin gaggawa wajen gudanar da aikin ceto.

Advertisement

An kama direban motar tare da miƙa shi ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike kan musabbabin hatsarin da kuma yiwuwar gurfanar da shi a kotu.

 

Advertisement

 

DAILY POST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending