Connect with us

News

Kofar Sulhu Ga Tubabbun ‘Yan Bindiga A Bude Take — Gwamna Radda

Published

on

Majalisar dokokin Jihar Katsina ta amince da ƙirƙiro gundumomi guda shida a jihar

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda, ya janye daga kan matsayarsa ta baya na rashin yin sulhu da ‘yan bindiga da ke addabar al’ummomin jihar, inda ya bayyana cewa a halin yanzu kofarsa ta tattaunawa a bude ta ke ga duk wanda ke son zaman lafiya.

Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar a shirye take ta karbi ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane wadanda su ka fito fili su ka mika wuya da zubar makamansu na ayyukan ta’addanci, inda ya ce gwamnati za ta taimaka musu wajen sa ke dawo da su cikin al’umma.

Advertisement

Gwamnan Kano Ya Yi Sabbin Naɗe-Naɗe Da Sauye-Sauyen Mukamai A Gwamnatinsa

Ya bukaci da su yi watsi da tashe-tashen hankula, su rungumi tattaunawa, tare da mika makamansu domin samar da zaman lafiya da ci gaba.

Advertisement

Gwamnan ya bayyana hakan ne ya yin kaddamar wa da mika gidaje 152 ga ‘yan gudun hijira a karamar hukumar Jibia da ke jihar a yau Alhamis.

An gina gidajen ne a karkashin shirin UNDP Northwest Prevention Facility Project a karkashin tallafin gwamnatin Jamus tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar.

Advertisement

Gwamnan ya bukaci wadanda har yanzu ke aikata miyagun laifuka da su dawo ga iyalansu da al’ummarsu, yana mai ba su tabbacin cewa gwamnati za ta iya ba su goyon baya da dama idan su ka zabi hanyar zaman lafiya ya yin da su ka ajiye makamansu, inda ya ce daga lokacin da su ka ajiye makamansu, za su iya amfana da tallafi irin wanda ‘yan gudun hijirar su ka samu.

Ya kuma bukace su da su zabi makomar ‘ya’yansu maimakon makamai, su zabi ci gaba maimakon barna, Ya ce za su iya samun gidaje, tallafin kudi, da sauran damarmaki ta hanyar zaman lafiya, kyakkyawan shugabanci, aiki na gaskiya, ba ta hanyar tsoratarwa ko zubar da jini ba.

Advertisement

Radda ya nanata kudurin gwamnatinsa na bin doka da oda da nufin kawo karshen matsalar rashin tsaro da ke addabar al’ummomi da dama a fadin jihar.

Ya ce zaman lafiya mai dorewa ya kasance mai matukar muhimmanci ga ci gaban jihar, ya kuma yi alkawarin ci gaba da tallafawa ayyukan da ke inganta zaman lafiya, gyara da kuma farfado da al’umma.

Advertisement

 

 

Advertisement

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending