Connect with us

News

Mutane 11 Sun Kamu Da Cutar Ƙwalara A Filato, Biyar Sun Rasu

Published

on

kadugen Kaduna Hospital (1)

Akalla mutum biyar ne suka rasa rayukansu sakamakon ɓarkewar annobar ƙwalara a Jihar Filato, yayin da hukumomin lafiya suka tabbatar da kamuwar wasu mutum 11 da cutar a sassa daban-daban na jihar.

Bullar cutar ta haddasa fargaba a tsakanin al’umma, musamman a yankunan da aka samu waɗanda suka kamu, lamarin da ya sa hukumomi suka ƙara zage damtse wajen hana yaɗuwarta.

Advertisement

Gwamnan Kano Ya Dakatar Da Shugabar  KNUPDA

Hukumar Kula da Lafiya ta Jihar Filato ta ce ta fara aiwatar da matakan gaggawa domin dakile annobar, inda ta ƙarfafa wayar da kan jama’a kan muhimmancin tsaftar muhalli, amfani da tsaftataccen ruwan sha da kuma gaggauta neman kulawar likita idan aka fara ganin alamun cutar.

Advertisement

Jami’an lafiya sun bayyana cewa ƙwalara cuta ce mai saurin yaɗuwa wadda ake kamuwa da ita ta hanyar shan gurbataccen ruwa ko cin abinci marar tsafta. Sun ce cutar na haddasa amai da gudawa mai tsanani, wanda kan janyo rashin ruwa a jiki cikin ɗan ƙanƙanin lokaci idan ba a samu magani da wuri ba.

A sakamakon haka, mahukuntan jihar sun buƙaci mazauna yankunan da abin ya shafa da su kula da tsaftar muhalli, su riƙa wanke hannu da sabulu akai-akai, tare da guje wa amfani da ruwan da ba a tabbatar da tsaftarsa ba domin rage haɗarin kamuwa da cutar.

Advertisement

 

 

Advertisement

LEADERSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending