News
Za’a fuskanci Katsewar Wutar Lantarki A Kano Da Wasu Jihohi A Ranar Lahadi

Kamfanin Sufurin Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar cewa za a samu katsewar wutar lantarki a wasu sassan Arewa a ranar Lahadi, 28 ga Yunin 2026, domin gudanar da aikin gyaran cibiyar rarraba wutar lantarki.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na TCN, Ndidi Mbah, ya fitar, ya ce aikin gyaran na da nufin inganta yadda ake rarraba wutar lantarki a yankunan da abin ya shafa.
Yadda jami’an Ƴansanda Sun Kama Wani Fasinja Da Ya Ɓoye Bindiga A Cikin Burodi
A cewarsa, katsewar za ta shafi masu amfani da wuta lantarki da kamfanin KEDCO ke kula da su, da kuma wasu sassan kamfanonin rarraba wuta na Jos (JEDC), Yola (YEDC) da Yobe (YEDC).
Jihohin da za su fi fuskantar katsewar sun haɗa da Kano, Katsina, Jigawa, da garin Azare a jihar Bauchi, da Nguru a jihar Yobe, har ma da Gazaoua a Jamhuriyar Nijar.
TCN ta nemi afuwar al’ummomin da lamarin zai shafa, tare da tabbatar da cewa za a dawo da wutar lantarki nan da nan bayan an kammala aikin gyaran.
