News
Jami’ar Northwest Kano Ta Kori Dalibai 34 Saboda Laifin Satar Amsa Lokacin Jarabawa

Hukumar gudanarwar Jami’ar Northwest University Kano (NWUK) ta amince da korar dalibai 34 daga jami’ar bayan samunsu da hannu a laifukan da suka shafi satar amsa lokacin jarabawa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Abubakar Ibrahim ya sanya wa hannu a madadin Magatakardar jami’ar, Dr. Adm. Isyaku Adamu.
Indai Dakarun Soji Da Yansanda Sun Kasa, Yansandan Jahohi Ma Ba Abunda Zasu Iya —Buba Galadima
Sanarwar ta bayyana cewa, an yanke wannan hukunci ne a yayin taron hukumar gudanarwar jami’ar karo na 66 da aka gudanar a ranakun 17 da 18 ga watan Yunin 2026, lokacin da ake nazarin sakamakon jarabawar zangon karatu na biyu na shekarar karatu ta 2024/2025.
Ta ce an dauki matakin ne bisa tanade-tanaden dokokin gudanar da jarabawa da ke kunshe a cikin kundin dokokin dalibai na jami’ar.
Baya ga korar daliban 34, hukumar gudanarwar ta kuma amince da dakatar da wasu dalibai 18 daga karatu na wani lokaci saboda irin wadannan laifuka, yayin da aka bai wa dalibai 22 takardun gargadi kan laifukan da suka shafi jarabawa.
Hakazalika, sanarwar ta ce an wanke wata daliba mai suna Rukayya Ahmad Zukuri daga dukkan zarge-zargen da ake yi mata bayan sake duba lamarin.
Jami’ar ta sake jaddada kudirinta na tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin ilimi, tare da gargadin dalibai da su kiyaye dokoki da ka’idojin gudanar da jarabawa, tana mai cewa duk wanda aka samu da karya dokokin zai fuskanci hukuncin da ya dace.
