News
Gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule Ya Sauke Kwamishinoninsa Guda 6
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sauke kwamishinoninsa guda shida daga kan muƙamansu, a wani ƙwarya-ƙwaryar garambawul da ya yi domin ƙara inganta gwamnatinsa.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Labaran Magaji, shi ya sanar da hakan yayin wani ƙarin haske ga ƴan jaridu bayan tashi daga zaman majalisar zartarwar jihar a ranar Talata,
Uba Ya Rasa Ransa Yayin Ƙoƙarin Ceto ‘Yarsa Da Ta Faɗa Rijiya A Kano
Magaji ya ce kwamishinonin da lamarin ya shafa sun haɗar dana Ma’aikatun Ayyuka, Harkokin Mata, Yaɗa Labarai, Ƙasa, Kimiyya da Fasaha, da kuma Ma’aikatar Tsaro.
Ya kuma bayyana cewa sauke sun ba wai yana nuna sun gaza gudanar da ayyukansu ba ne, kuma majalisar zartarwar ta yaba da ƙwazonsu da jajircewa a lokacin gudanar da ayyukan nasu.
Magaji ya ce za a ci gaba da damawa da tsoffin kwamishinonin a gwamnatin jihar, za kuma a iya ba su jagorancin wasu ayyukan. Ya kuma ce za a sanar da sunayen sabbin kwamishinonin da za a naɗa nan ba da jimawa ba.
-
Opinion4 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion3 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News4 days ago
Jihar Kano Ta Shiga Jerin Jahohi 10 Mafi Tara Kudaden Shiga Na VAT A 2026
