News
Uba Ya Nemi Kotu Ta Tilasta Wa ’Yarsa Ta Fitar Da Mijin Aure A Kaduna
Wani magidanci mai suna Lawal Hamisu ya shigar da ƙara a gaban Kotun Shari’a ta II da ke Magajin Gari a Jihar Kaduna, inda yake neman kotu ta umarci ’yarsa, Fatima Lawal, ta gabatar da mutumin da zai aure ta.
Ta bakin lauyansa, H.B. Debo, mai ƙarar ya shaida wa kotun cewa Fatima mai shekara 27 ta kammala karatun Babbar Difloma ta Ƙasa (HND), amma har yanzu ba ta gabatar da wani mutum da ya nemi aurenta a hukumance ba.
ICPC Ta Gano Ma’aikatan Bogi 908 A Wasu Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya 50
Lawal ya ce duk da cewa ’yarsa tana da samari, babu wanda ya taɓa zuwa gidansu domin neman aurenta. Ya buƙaci kotun ta umarce ta da ta fito da wanda zai aure ta, sannan ta taimaka wajen ganin an ɗaura auren idan an cika sharuddan da suka dace.
Ya kuma yi zargin cewa mahaifiyar Fatima ce ta haddasa matsalar da ke tsakaninsa da ’ya’yansa.
A nata ɓangaren kuwa, Fatima ta musanta cewa tana da wanda ya nemi aurenta, tana mai cewa duk da kasancewar tana da abokai maza, babu wani da ya gabatar da kansa ga iyayenta a matsayin mai neman aurenta.
Da yake jawabi, Alƙalin kotun, Malam Yakubu Abdullahi, ya bayyana cewa shari’ar ta shafi dangantakar uba da ’yarsa, don haka tana buƙatar a yi taka-tsantsan kafin a yanke hukunci.
Alƙalin ya ce zai saurari kowanne ɓangare daban domin gano ainihin musabbabin rikicin kafin ya yanke hukunci.
Daga nan kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 3 ga Agusta, 2026.
-
Opinion4 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion4 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News4 days ago
Jihar Kano Ta Shiga Jerin Jahohi 10 Mafi Tara Kudaden Shiga Na VAT A 2026
