News
Gwamnatin Tarayya Ta Ba Jami’o’i Da Kwalejoji Umarnin Korar Ɗalibai Da Ke Da Alaka Da Laifin Garkuwa Da Mutane
Gwamnatin Tarayya ta umarci shugabannin jami’o’i, kwalejojin kimiyya da fasaha da kwalejojin ilimi a faɗin Nijeriya da su kori duk ɗalibin da aka tabbatar, bayan cikakken bincike, da hannu a aikata laifin garkuwa da mutane ko wasu laifuka masu alaƙa da hakan.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya ba da wannan umarni yayin da ya karɓi shugabannin Majalisar Gudanarwa da mahukuntan Jami’ar Tarayya ta Lafia a Abuja.
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
A cikin wata sanarwa da Mai Ba Ministan Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Sadarwa, Ikharo Attah, ya fitar, Alausa ya ce bai kamata cibiyoyin ilimi su zama mafakar masu aikata laifuka ba, yana mai jaddada cewa duk wanda aka samu da hannu a irin waɗannan munanan ayyuka ba shi da gurbi a manyan makarantun ƙasar.
Ya ce, “Idan aka ci gaba da kyale munanan ɗabi’u, za su zama al’ada. Duk ɗalibin da aka tabbatar da laifin shirya ko shiga garkuwa da ɗalibai takwarorinsa, dole ne a kore shi daga makaranta.”
Ministan ya kuma umarci shugabannin manyan makarantu da su ƙarfafa tsarin tattara bayanan sirri a harabar makarantu tare da faɗaɗa haɗin gwiwa da Hukumar Tsaro ta DSS da sauran hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin ɗalibai.
A cewarsa, duk da cewa jami’o’i da kwalejojin Nijeriya na ci gaba da kasancewa cikin yanayi mai kyau ta fuskar tsaro, wasu al’amuran da suka faru a baya-bayan nan sun nuna akwai buƙatar ƙara ɗaukar matakan kariya, musamman wajen hana aikata laifuka a ciki da wajen harabar makarantu.
Har ila yau, Alausa ya bayyana cewa ya tattauna da Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), kan yadda za a ƙarfafa shirin Safe Schools Initiative domin inganta tsaro da kare ɗalibai a faɗin ƙasar.
Ministan ya kuma yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan goyon bayan da yake bai wa hukumomin tsaro da kuma sauye-sauyen da gwamnatin ke aiwatarwa a fannin ilimi, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da tabbatar da cewa ɗalibai suna samun ilimi cikin yanayi mai aminci.
-
News6 days ago
Gwamnatin Kano Ta Umarci Masu Talla Da Masu Sana’ar Jari Bola Su Bar Karkashin Gadar Tal’udu
-
News3 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
