Connect with us

News

WAEC Ta Rike Sakamakon Jarrabawar Dalibai 167,486

Published

on

Da Ɗumi ƊumiWAEC ta Fitar Da Sakamakon Jarabawar WASSCE Ta 2024

Hukumar Shirya Jarrabawar Ƙasashen Yammacin Afirka (WAEC) ta sanar da riƙe sakamakon ɗalibai 167,486 da suka rubuta jarabawar kammala makarantar sakandare ta WASSCE ta shekarar 2026, sakamakon zargin hannu a maguɗin jarrabawa.

Hukumar ta ce adadin da aka riƙe sakamakonsa ya kai kashi 8.59 cikin ɗari na jimillar ɗaliban da suka zauna jarabawar, wadda aka gudanar ta hanyar amfani da kwamfuta (CBT). Sai dai WAEC ta bayyana cewa wannan adadi ya ragu idan aka kwatanta da kashi 9.7 cikin ɗari da aka samu a shekarar 2025.

Bayan Watanni Shida, An Ceto Mutane 176 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kwara

Shugaban Ofishin WAEC na Ƙasa a Nijeriya, Dr. Amos Dangut, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin taron sanar da sakamakon jarabawar da aka gudanar a birnin Legas.

A cewarsa, an riƙe sakamakon waɗanda abin ya shafa ne domin ci gaba da bincike kan zargin aikata maguɗin jarrabawa. Ya ce daga cikin dalilan da suka haddasa hakan akwai amfani da wayoyin hannu a ɗakunan jarrabawa duk da haramcin da aka sanya, da kuma zargin shirya maguɗi cikin haɗin gwiwa a wasu cibiyoyin rubuta jarabawa.

Dr. Dangut ya tabbatar da cewa hukumar za ta gudanar da cikakken bincike kan dukkan shari’o’in da suka shafi maguɗin jarrabawa kafin ta yanke hukunci kan sakamakon ɗaliban da abin ya shafa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending