Connect with us

News

WASSCE 2026: Kashi 61.5 Cikin 100 Na Ɗalibai Sun Samu Darussa Biyar Har Da Turanci Da Lissafi

Published

on

WAEC Ta Sanar Da Sabon Tsarin Gyara Jarrabawar Da Mutum Ya Fadi Ba Sai Ya Yi Jiran Shekara Daya Ba

Hukumar Shirya Jarabawar Afirka ta Yamma (WAEC) ta bayyana cewa kashi 61.5 cikin 100 na ɗaliban da suka rubuta jarabawar kammala sakandare ta WASSCE ta shekarar 2026 sun samu aƙalla darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi, abin da ke nuna ingantuwar sakamakon jarabawar bana.

A cewar hukumar, sama da ɗalibai miliyan 1.2 ne suka cimma wannan nasara, yayin da aka riga aka fitar da sakamakon kusan kashi 94 cikin 100 na dukkan waɗanda suka zauna jarabawar. WAEC ta ƙara da cewa ana ci gaba da tantancewa da kammala sakamakon sauran ɗaliban da har yanzu ba a fitar da nasu ba.

NSCDC Ta Hukunta Jami’ai 79 Tare Da Sallamar 37 Kan Zargin Rashawa Da Sata

Hukumar ta bayyana cewa an gudanar da dukkan matakan tantance sakamakon ne cikin tsauraran matakan tabbatar da inganci da gaskiya, tare da alƙawarin fitar da sauran sakamakon da zarar an kammala bincike da tantancewar da ake yi.

Sakamakon na bana ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ƙoƙarin inganta tsarin gudanar da jarabawa da rage magudin jarrabawa, lamarin da masana ilimi ke ganin zai taimaka wajen ƙara darajar takardun WAEC a Najeriya da sauran ƙasashen Afirka ta Yamma.

Masu ruwa da tsaki a fannin ilimi na sa ran wannan sakamako zai ƙarfafa ɗalibai da makarantu su ƙara himma wajen neman ilimi, tare da ci gaba da inganta matakan koyarwa da koyo a faɗin ƙasar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending