News
Shugaba Tinubu Ya Umurci EFCC Ta Bude Asusun Bankin Gwamnatin Jihar Osun Da Ta Kulle
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umurci Hukumar EFCC da ta gaggauta komawa kotu domin janye umarnin da ta samu na dakatar da asusun gwamnatin jihar Osun.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Tinubu ya ce ko da yake bai saba tsoma baki cikin ayyukan hukumomin yaki da cin hanci ba, ya damu da lokacin da aka bijiro da matakin ba, kasancewar jihar Osun na gab da gudanar da zaben gwamna.
Shugaban ya ce bai san da matakin EFCC tun da farko ba, amma ya yi gargadin cewa bai kamata a dauki wani mataki da zai iya haifar da zargin cewa gwamnatin tarayya na kokarin yin tasiri kan zaben ba.
Saboda haka, ya ce ya umurci EFCC da ta janye umarnin kotun tare da dakatar da duk wani mataki da ta dauka kan gwamnatin jihar Osun domin kare mutuncin tsarin dimokuradiyya.
-
News4 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News2 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
