News
NDLEA Ta Kama Matashi Mai Shekaru 20 Da Kwayoyin Pregabalin 785,000 a Kano
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kama wani matashi mai shekaru 20, Saidu Adamu, da ake zargi da safarar capsules 785,000 na Pregabalin a Kano.
Hukumar ta ce nauyin ƙwayoyin sun kai kilogiram 669.425, inda aka kama matashin a wani samame da jami’an NDLEA suka gudanar a Sabon Gari, cikin birnin Kano.
Rikicin Boko Haram Ya Lalata Makarantu Fiye Da 5,000 A Borno —Gwamnan Zulum
Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na NDLEA, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a hedikwatar hukumar da ke Abuja.
A wani samamen daban, jami’an hukumar sun kama ƙwayoyin Diazepam guda 1,700 da aka ɓoye a cikin burodin da ake safara a kan hanyar Zariya–Kano–Hadejia.
Sanarwar ta ce an kama wani mutum mai shekaru 28, Habibu Sabitu, a yayin aikin binciken ababen hawa da jami’an hukumar suka gudanar a kan hanyar.
