News
Gamayyar Kungiyoyin Fararen Hula Sun Buƙaci Shugaba Tinubu Ya Shiga Tsakani Kan Rikicin Siyasar Kano
Gamayyar Ƙungiyoyin Fararen Hula ta Kano (Kano Patriotic CSOs Coalition Forum – KPCF) ta yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta shiga tsakani kan abin da ta bayyana a matsayin ƙara ɗumamar yanayin siyasa da zamantakewa a Jihar Kano.
Ƙungiyar ta yi wannan kiran ne cikin wata wasiƙa da ta aika wa Shugaba Tinubu a ranar 8 ga Oktoban 2026, inda ta ce jihar na cikin wani yanayi da ke buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin hana tashin hankali da ka iya rikidewa zuwa rikici.
ASUU-KUST Ta Yabawa Gwamnatin Kano Kan Aiwatar Da Yarjejeniyar 2025
KPCF ta ce yanayin ya ƙara tsananta ne sakamakon yadda harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi, da kuma takaddamar da ta shafi masarautar Kano.
Ƙungiyar ta kuma bayyana damuwarta kan wata magana da ta ce an danganta wa Alhaji Aminu Babba Dan’agundi, Sarkin Dawaki Babba, tare da wasu abubuwan da ta ce suna buƙatar kulawar hukumomin da abin ya shafa.
Haka kuma, KPCF ta yi tsokaci kan wani faifan bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, wanda ake zargin ɗan takarar NDC na Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Gwale, Aminu Abdullahi Warkal, yana riƙe da wani makami da ake zargin bindigar pump-action ce a wani taron siyasa.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta gayyaci Warkal zuwa hedikwatarta da ke Bompai domin yi masa tambayoyi, yayin da bincike kan lamarin ke gudana. Rundunar ta ce idan aka tabbatar da zargin, hakan na iya zama saɓa wa dokar mallakar bindigogi tare da barazana ga zaman lafiyar jama’a.
KPCF ta kuma nuna damuwa kan wani taron Durbar da aka shirya na Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, inda ta ce an samu rahotannin tashin hankali yayin taron.
A cewar ƙungiyar, an lalata wasu fastoci da allunan tallan siyasa masu ɗauke da hotunan Shugaba Tinubu da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
KPCF ta ce ta samu rahotannin cewa daga bisani Sarkin ya nemi afuwar Gwamna Abba Kabir Yusuf, tana mai cewa irin wannan mataki na iya taimakawa wajen rage zafin da ake ciki.
Sai dai ƙungiyar ta buƙaci hukumomin da abin ya shafa su gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin abin da ya faru, tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi bisa tanadin doka.
KPCF ta kuma yi kira ga jami’an gwamnati da ’yan siyasa a matakin tarayya da na jiha da su guji kalamai ko matakan da za su iya ƙara rura wutar rikici ko kuma nuna bangaranci kan batutuwan masarautar Kano da ke gaban kotu.
Ta buƙaci a bai wa ɓangaren shari’a damar gudanar da aikinsa cikin ’yanci ba tare da matsin lamba ko tsoratarwa ba, tare da kira ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa da su mutunta tsarin shari’a da hukuncin kotuna.
Daga cikin buƙatun da KPCF ta gabatar wa Shugaba Tinubu akwai umartar hukumomin tsaro da na leƙen asiri da su ƙara sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a Kano, tare da ɗaukar matakan kariya daga tashin hankali, barazana, kalaman ƙiyayya da lalata dukiyoyi.
Ƙungiyar ta kuma nemi a bai wa dukkan jam’iyyun siyasa da magoya bayansu kariya ba tare da nuna bambanci ba, tare da gudanar da bincike kan lalata kayan yakin neman zaɓe da kuma hukunta duk wanda aka samu da hannu wajen aikata tashin hankali, ba tare da la’akari da matsayinsa na siyasa ko na gargajiya ba.
Haka kuma, KPCF ta ba da shawarar gudanar da tattaunawar zaman lafiya da za ta haɗa Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jihar Kano, sarakunan gargajiya, jam’iyyun siyasa, hukumomin tsaro, malaman addini, matasa, mata da ƙungiyoyin fararen hula.
Ƙungiyar ta ce Kano na da matuƙar muhimmanci ga Najeriya saboda kasancewarta babbar cibiyar kasuwanci, al’adu, siyasa da zamantakewa, tana mai cewa duk wani rikici a jihar na iya yin tasiri a sauran sassan Arewa da ma ƙasar baki ɗaya.
KPCF ta yi kira ga dukkan ɓangarorin da su fifita zaman lafiya da haɗin kan al’ummar Kano a kan muradun siyasa da na kashin kai.
“Kano ta kowa ce,” in ji ƙungiyar, wadda ta buƙaci Shugaba Tinubu da ya yi amfani da matsayinsa da ikon da Kundin Tsarin Mulki ya ba shi wajen tabbatar da zaman lafiya, dimokuraɗiyya, ’yancin faɗar albarkacin baki, mutunta hukumomin gargajiya da bin doka.
-
News5 days ago
Matasa A Unguwar Gama Sun Yi Kira Ga Majalisar Dokokin Kano Ta Ladabtar Da Ɗan Majalisar Nassarawa Kan Zargin Cin Zarafin Gwamna
-
News6 days ago
Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Dawo Da Tallafin Man Fetur Ba Kuma Ba Ya Da-na-sanin Cire Shi
-
News5 days ago
DSS Ta Gurfanar Da Mutum Biyar Gaban Kotu Bisa Zarginsu Da Garkuwa Da ‘Yan NYSC 20 A Imo

