Connect with us

News

Kasuwar ‘yan ƙwallo: Makomar Jesus, Salah, Mbappe, Navas, Rice, Dumfries

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Arsenal na son dauko ɗan wasan Manchester City Gabriel Jesus, mai shekara 25, zuwa Emirates, tuni kuma wakilan ƙungiyar suka soma tattaunawa da ɗan wasan dan asalin Brazil.(Athletic, subscription required)

Advertisement

Mo Salah na son ci gaba da zama a Liverpool sai dai akwai rashin tabbas kan makomarsa a gaba ganin har yanzu ba a cimma yarjejeniya ba kan kwantiraginsa, kuma ɗan wasan mai shekara 29 asalin kasar Masar na cewa Kudi ba ita kadai ba ce abin dubawa. (Four Four Two)

Paris St-Germain ta gabatar da tayin euro miliyan 50 kan ɗan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 23 a shekara, hakan zai sa ya kasance ɗan wasa mafi tsada a ƙungiyar. Akwai ɗan matsalar kan batun komawarsa Real Madrid kan abin da ya shafi ‘yanci. (Goal)

Advertisement

Mahaifiyar Mbappe da wakilinsa Fayza Lamari na tattaunawa a Qatar da mai kungiyar PSG(Le Parisien – in French, subscription required)

Kocin Tottenham Antonio Conte ya matsu ya koma horar da PSG a kaka ta gaba kuma yana da kwarin-gwiwar zai iya maye gurbin Mauricio Pochettino a Parc des Princes. (Le Parisien – in French, subscription required)

Advertisement

Newcastle na shirin daukan mai tsaron ragar PSG Keylor Navas, wanda zai yi bankwana da kungiyar da ke jan ragama a Ligue 1a wannan kakar, sai dai ɗan wasan mai shekara 35 asalin Costa Rica ya lasawa Juventus da Sevilla zuma a baki. (Fichajes – in Spanish)

Declan Rice ya sake yin watsi da tayin West Ham karo na uku kan albashin £200k a kowanne mako. Duk da cewa ƙungiyar ta dage kan cewa ɗan wasan ba na sayarwa ba ne za ta iya karban fam miliyan 150 kan ɗan wasan mai shekara 23 daga hannun masu farautarsa Manchester United da Chelsea(The Guardian)

Advertisement

Tottenham ta tattauna da Inter Milan kan saye ɗan wasan Netherlands Denzel Dumfries, mai shekara 26. (Tuttosport, via Sport Witness)

Celtic ta shiga wani mataki a tattaunawarta da Tottenhamkan saye ɗan wasanta na baya Cameron Carter-Vickers, mai shekara 24. (SBI Soccer)

Advertisement

An sanar da wani ɗan wasan TottenhamJoe Rodon mai shekara 24, cewa yana iya barin kungiyar. (Football Insider)

Newcastle na bibiyar ɗan wasan Monaco Benoit Badiashile, da kuma na Bayer Leverkusen Moussa Diaby, mai shekara 22. (Foot Mercato)

Advertisement

Ɗan wasan Chelsea Antonio Rudiger ya nuna cewa babu batun tafiya Manchester United(Ben Jacobs, CBS)

Wayne Rooney ya yi watsi da tayin Erik ten Hag da ke son su yi aiki tare a Manchester United, ya dage kan cewa zai iya barin Derby County ne kaɗai domin aikin horaswa. (Athletic, subscription required)

Advertisement

Fulham na son dauko dan wasan Lazio Sergej Milinkovic-Savic mai shekara 27.. (90 Min)

Tsohon ɗan wasan Manchester UnitedWest Ham da Manchester City Carlos Tevez na iya bada mamaki ya dawo fagen tamaula bayan shekara guda, rabon ɗan wasan mai shekara 38 ya taka leda tun wasan da ya bugawa Boca Juniors. Dan wasan mutumin Argentine ya ziyarci AC MilanJuventus da Tottenham da kuma kungiyarsa West Ham. (Goal)

Advertisement

Leicester da Aston Villa na zawarcin tsohon ɗan wasan Manchester City da Fulham loanee Seko Fofana, mai shekara 26. Ɗan kasar na Ivory Coast yanzu haka na zaman aro a Lens(But! Football Club)

Barcelona ta kawar da wata alamar za ta tuntubi ɗan wasan Arsenal Gabriel Magalhaes, mai shekara 24, saboda dalilai na kudi. (Mundo Deportivo)

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending