Connect with us

Sports

Man City ta lashe Premier League karo na shida

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Manchester City ta lashe kofin gasar Premier League ta Ingila karo na shida bayan ta farke ƙwallo biyu Aston Villa ta zira mata a filin wasa na Etihad.

Advertisement

Ƙungiyar da Pep Guardiola ke jagoranta ta ƙare kakar ta bana da tazarar maki ɗaya kacal tsakaninta da Liverpool, wadda ta doke Wloves 3-1 a wasan ƙarshe a yau.

Ƙwallo biyu da Ikay Gundogan ya ci da kuma wadda Rodri ya zira a cikin minti shida kacal su ne suka bai wa City nasara inda ta lashe wasan da 3-2.

Advertisement

Villa ta shiga gaba a wasan tun farko ta hannun Matty Cash da Philippe Coutinho.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending