Connect with us

Sports

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar de Jong, Tchouameni, Leao, Harry Kane, Mkhitaryan, Doucoure da Torreira

Published

on

 

Daga mujahida danlami Garba 

Advertisement

 

 

Advertisement

Manchester United ta shaida wa dan wasan tsakiya na Barcelona da Netherlands Frenkie de Jong, mai shekara 25, cewa za su karkata akalarsu zuwa wani waje idan ya kasa yanke shawara ko yana son zuwa Old Trafford a bazara. (Sport Spanish)

Shirin dan wasan tsakiyar Monaco Aurelien Tchouameni na komawa Real Madrid ya tsaya ciki saboda batun haraji. Zakarun La Liga sun shirya biyan kusan Yuro miliyan 80 (£68m) kan dan wasan na Faransa mai shekaru 22. (ESPN)

Advertisement

Manchester United, da Liverpool, da Arsenal da Chelsea duk suna zawarcin Tchouameni (Sun)

AC Milan na son kulla yarjejeniya da dan wasan gaban Portugal Rafael Leao, mai shekara 22, kan sabuwar yarjejeniya domin hana Real Madrid zawarcinsa. Kungiyar ta Spaniya na neman dan wasan gaba bayan dan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 23, ya yanke shawarar ci gaba da zama a Paris St-Germain. (La Gazzetta dello Sport)

Advertisement

Dan wasan Everton Richarlison, mai shekara 25, zai iya barin Goodison Park a wannan bazarar yayin da Tottenham, da Real Madrid da Paris St-Germain ke zawarcinsa (Mail)

Everton na fafatawa da West Ham don sayen dan wasan gaban Burnley da Ivory Coast Maxwel Cornet, mai shekara 25, bayan ta fice daga gasar Premier. (Telegraph)

Advertisement

Kyaftin din Tottenham Harry Kane a shirye yake ya fara tattaunawa kan sabon kwantaragi da kungiyar, duk da cewa dan wasan na Ingila mai shekaru 28 ya matsa kaimi zuwa Manchester City a bazarar da ta gabata. (Evening Standard)

Inter Milan na fatan daukar Henrikh Mkhitaryan, mai shekara 33, lokacin da kwantiraginsa da Roma zai kare a bazara. Dan wasan tsakiyar na Armeniya yana kuma tunanin tayin da kungiyar da ta lashe gasar ta Europa ta sake yi masa. (Fabrizio Romano)

Advertisement

 

Kashi-kashi
End of Podcast
Arsenal na zawarcin dan wasan tsakiyar Lens Cheick Doucoure dan kasar Mali, mai shekara 22. Sai dai kuma suma Brighton, da Everton, da Crystal Palace da Wolves suma suna zawarcinsa (Mirror)

Advertisement

Leicester City na shirin bai wa dan wasan baya na Ireland ta Arewa Jonny Evans, mai shekara 34, sabon kwantiragin shekara guda. Amma za su saurari tayin dan wasan bayan Denmark Jannik Vestergaard, mai shekara 29, da dan wasan tsakiya na Faransa Boubakary Soumare, mai shekara 23, yayin da Brendan Rodgers ke kokarin yi wa kungiyar garambawu. (Mail)

Manchester United na iya yin tayin sayen Christopher Nkunku da Liverpool da Chelsea ke nema a mako mai zuwa, yayin da dan wasan gaban Faransar mai shekara 24 ya hakura ya kulla sabuwar yarjejeniya da RB Lepizig. (Florian Pettenberg)

Advertisement

Paris St-Germain ba za ta sayi dan wasan gefe na Barcelona Ousmane Dembele, mai shekara 25 ba, a bazarar nan duk da cewa ana alakanta dan wasan na Faransa da komawa kasarsa ta haihuwa. (Le Parisien)

Fiorentina na fafutukar ganin sun amince da cinikin dan wasan tsakiyar Arsenal Lucas Torreira. Dan wasan tsakiyar na Uruguay, mai shekara 26, ya burge kungiyar ta Italiya yayin da yake zaman aro (Evening Standard)

Advertisement

Manchester United ta tattauna da sabon kocinta Erik ten Hag game da dan wasan bayan Ajax na Netherlands Jurrien Timber, mai shekara 20, da kuma dan wasan Villareal na Spain Pau Torres, mai shekara 25. (Caught Offside)

Wani mai yi wa Paul Pogba aiki ya jefa wani bayani a shafin Instagram game da makomar dan wasan tsakiyar mai shekara 29, yana mai nuni da cewa dan wasan na Faransa zai koma Juventus idan kwantiraginsa a Manchester United ya kare a bazara. (Manchester Evening News)

Advertisement

West Ham za ta saurari tayin dan wasan tsakiyar Jamhuriyar Czech, Tomas Soucek, mai shekara 27, a wannan bazarar sakamakon rashin jituwa da kocinta David Moyes. (Football Insider)

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending