News
Biden da Putin za su yi ganawar ƙeƙe da ƙeƙe Biden da Putin
Shugaba Joe Biden na Amurka da Vladimir Putin za su sake zantawa ta wayar tarho a yau Alhamis yayin da Amurka ke kokarin hada kai da kasashen Turai wajen daukar mataki iri daya game da kara tura dakaru zuwa iyakarta Ukraine da Rasha ke yi.
Wani babban jami’i a gwamnatin Biden ya ce mutanen biyu za su tattauna batutuwa daban-daban na tsaro kuma Amurka a shirye take ta tattauna da Rasha game da damuwar da take da.
Jami’in ya ce Washington shirye take da a nemo mafita ta hanyar diflomasiyya; amma tare da haka, shirye take ta mayar da martani da tsauraran takunkumai idan Moscow ta mamaye Ukraine.
Shugabannin biyu dai sun wani taro ta na’ura a wannan watan wanda a ciki Mr. Biden ya sake jaddada goyon bayansa ga ci gaba da kasancewar Ukraine kasa mai cikakken ‘yanci.