News
Ƙasar Saudiya tace zata cire takunkumin da ta saka wa Nigeriya domin Alhazai su samu damar gabatar da aikin hajji a kasa mai tsarki
Daga Kabir basiru fulatan
Jakadan Saudiyan na Nigeriya Faisal Bin Ibrahim Al-Ghamidy ya bada haske akan haka yayin wata ziyara da hukumar Aikin Hajji ta kai ofishin sa a Abuja.
Saudiya ta sanar da dakatar da jiragen Nigeriya shiga kasar ne a Watan Disambar 2021 saboda gujewa yaduwar cutar Omicron COVID-19.
Jakadan yace “Ina fatan dakatarwar shigar jirgin zuwa kasar Saudiya daga Nigeriya zai zo karshe.
Yayi maganar diyya ga ‘yan uwan wanda hadarin inji ya rutsa dasu a makka a shekarar 2015 wanda ya kashe mahajjata sama da d’ari.
Ya cigaba da cewa kasar shi zata tabbatar ta bayar da diyyar zuwa ga magadan wanda suka rasa ransu da kuma wakilan su idan sun gabatar da abinda ake bukata.
Shugaban hukumar Hajjin ta kasa NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan yayi godiya akan goyan baya da hadin kan da kasashen biyu suke dashi.