Connect with us

News

Binciken Gaskiya: Da gaske CBN ya rage kuɗin da bankuna ke cazar ‘yan Najeriya?

Published

on

123110435 gettyimages 622347656 594x594.jpg
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddini

Wasu rahotanni da jaridu a Najeriya suka wallafa ya yi iƙirarin cewa Babban Bankin Najeriya CBN ya umarci bankuna da su rage cajin da suke yi wa ‘yan ƙasar wajen cira da kuma tura kuɗaɗe.

Sai dai wani binciken kamfanin dillancin labarai na AFP ya gano cewa umarnin ba sabo ba ne, cajin kuɗin da bankunan ke yi bai sauya ba.

Rahotannin rage cajin ba gaskiya ba ne kasancewar tun 2019 bankin ya fitar da jerin umarnin game da tura kuɗi ta intanet da kuma cire su ta na’urar ATM.

Advertisement

Cajin kuɗi bai sauya ba

Kawunan labarin da mutane suka yaɗa na nuna cewa kamar an rage yawan kuɗaɗen da ake caza ne sakamakon sabbin dokokin na CBN.

Binciken na AFP ya kwatanta dokokin CBN da aka wallafa a 2029 da na 2022, kuma ya gano cewa iri ɗaya ne. Dokokin na 2019 su ne dai suke aiki, inda suka maye gurbin na 2017 da 2013 da kuma na farko da aka samar a 200

Tun a 2018 ne ‘yan Najeriya suka fara ƙorafi da zanga-zanga a shafukan zumunta ƙarƙashin maudu’in #Reform9jabanks (a gyara bankunan Najeriya) da zimmar neman a daina ɗaukar musu kuɗaɗe, ciki har da N50 ta kula da katin ATM duk wata.

Advertisement

Bayan ‘yan majalisar ƙasar sun saka baki, sai CBN ya sake duba dokoin. An rage cajin cirar kuɗi ta ATM na bankin da ba na mutum ba, sannan aka rage cajin tura kuɗi ta intanet daga N300 zuwa N50 a matsayin mafi yawan adadi.

Bugu da ƙari, CBN ya cire kuɗin kula da ATM daga babban asusun ajiya wato current sannan ya rage caji a kan ƙaramin asusu wato savings zuwa N50 cikin wata uku maimakon a wata ɗaya.

Kuɗin kula da kati wato maintenance fee a Turance, shi ne kuɗin da kowane mai riƙe da katin ATM ke biya saboda ba shi kulawa da bankinsa ke yi.

Advertisement

“An cire caji a kan asusun current ne saboda da ma ana cirar kuɗin kula da asusun,” a cewar CBN.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *