News
Fadar Sarkin Kano ta kai ƙorafin Air Peace ga NCAA

Daga kabiru basiru fulatan
Fadar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ta rubutawa Hukumar kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Najeriya, NCAA, wasiƙar koke, inda ta nemi a hukunta kamfanin jirgin sama na Air Peace sabo da abin da ta kira da rashin girmama wa ga Sarki da mutanen Jihar Kano.
Daily Trust ta rawaito cewa Babban Hadimin Sarkin, kuma kawu gare shi, Isah Bayero, a cikin takardar koken da ya shigar gaban hukumar NCAA a jiya Alhamis, ya ce kamfanin jirgin ya jinkirta jigilar su daga Banjul zuwa Legas da sama da sa’a daya kuma ya hana su shiga jirgin da zai dawo da su Kano domin sun iso Legas saura minti 30 ya tashi.
Bayero ya ce, “Mu 10 ne har da Mai Martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da wasu fasinjojin na Musamman guda hudu tare da karin wasu fasinjoji masu guda biyar duk mun shiga jirgin Air Peace mai lamba P47776 da ya dawo daga Banjul zuwa Legas.
“An shirya tashin mu daga Banjul da karfe 00:10 na safe a ranar 24 ga Fabrairu, 2022, amma mun tashi daga Banjul da karfe 01:19 na safe, muka sauka a Legas da karfe 5:45 na safe. Da misalin karfe 6:15 jirginmu ya tashi zuwa Kano a dai jirgin na Air Peace”. Inji Isa pilot
Ya ce shi da kan sa ya kirawo Shugaban Kamfanin na Air Peace, Allen Onyeama, domin ya sanar da shi halin da ake ciki, ya kuma buƙace shi da ya taimaka ta hanyar jinkirta tashin su zuwa Kano, domin girmamawa ga mai martaba Sarkin Kano.
“A fili yace ya ƙi kuma ya sha alwashin cewa ba zai yi hakan ba. Ni da kaina na ɗauki wannan a matsayin cin fuska da kuma rashin mutunta mai martaba da ma al’ummar Kano baki daya.” inji takardar korafin.
Ya ce, duk da cewa sun kama otal ne kudinsu, kamfanin jirgin ya kuma bukaci su biya kudin “No-show” a lokacin da suke son sake tsara yadda jirgin gaba na kamfanin da zai zo da karfe 7 na dare.
“Wannan wani matsanancin hali ne na rashin hankali da rashin tausayi. Dangane da abin da ya gabata, na ji matukar bacin rai kuma ina neman ku yi abun da ya dace don daukar matakan da suka dace don hana faruwar hakan a nan gaba.,” in ji shi.
Da wakilin Jaridar Daily trust ya tuntubi mai magana da yawun kamfanin Inda ya ce zai binciki lamarin ,amma kuma har lokacin hada wannan rahoton bai tuntube shi ba.
Darakta-Janar na NCAA, Kyaftin Musa Nuhu, ya tabbatar da samun wasikar koken amma ya ki cewa komai.
“Zan iya cewa mun sami wasikar, kuma muna aikin akan ta amma ba zan iya cewa komai a kai ba,” in ji shi