Sports
Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Salah, Dybala, Kessie, Hazard, Jovic
Daga Kabiru basiru fulatan
Juventus na shirin samar da makudan kudade domin jan hankalin Mohamed Salah, dan wasan Liverpool dan asalin Masar mai shekara 29 zuwa Turin. (La Gazzetta dello Sport – in Italian)
Manchester United na duba yiwuwar dauko mai horas da ‘yan wasan Sevilla dan Spanish Julen Lopetegui, mai shekara 55, a daidai lokacin da suke ci gaba da laluben wanda zai maye gurbin kocinsu Ralf Rangnick na dindindin. (Marca – in Spanish)
Dan wasan tsakiya na Ivory Coast Franck Kessie, mai shekara 25, ya amince da kwantiragin shekara hudu da Barcelona, zai kuma fara wasa da Nou Camp a karshen kakar bana idan kwantiraginsa da AC Milan ya zo karshe. (Guardian)
Shi kuwa dan wasan Belgium, wato Eden Hazard yana cikin dimuwa da damuwa a Real Madrid, wadda take niyyar kawo karshen kwantiragin dan wasan mai shekara 31 a wannan kakar wasannin. (Goal)
-
News4 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News2 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News4 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
