Sports
Kasuwar ‘yan ƙwallo: Makomar Rashford, Rooney, Dybala, Osimhen, Tchouameni, Reguilon
Daga Khadija abdullahi muhmd
Arsenal ta gabatar da bukatarta ta sayen ɗan wasan gaba a Manchester United da Ingila Marcus Rashford, mai shekara 24. (Football Insider)
Kocin Derby Wayne Rooney shi ne kan gaba a cikin mutanen da Burnley ke son ganin ya maye gurbin kocin kungiyar kuma tsohon mai gidansa Sean Dyche. (Sun)
Sabon kocin Manchester United Erik ten Hag na son sayo ɗan wasa daga Juventus mai buga gaba a Argentina Paulo Dybala, mai shekara 28. (Corriere dello Sport – in Italian)
Manchester United ta nuna wa Napoli cewa a shirye take ta biya £84m kan ɗan wasanta dan Najeriya mai shekara 23 Victor Osimhen. (La Repubblica – in Italian)
Liverpool na duba yiwuwar dauko ɗan wasan Monaco mai shekara 22 dan asalin Faransa da ke buga tsakiya Aurelien Tchouameni. (Mail)
Tottenham za ta yi nazarci kan tayin da take samu kan ɗan wasanta dan kasar Sifaniya mai buga gefe Sergio Reguilon, mai shekara 25. (Football Insider)
Manchester United ta samu goron gayyatar gabatar da tayinta kan ɗan wasan Wolves‘ asalin Portugal mai buga tsakiya Ruben Neves, mai shekara 25. (Manchester Evening News)
Crystal Palace na duba yiwuwar dauko aron ɗan wasan Manchester United Aaron Wan-Bissaka. Matashin mai shekara 24 ya haska mata sau 42. (Athletic)
Napoli ta yanke hukunci kan saye ɗan wasan Manchester United Axel Tuanzebe a yarjejeniyar dindindin. Ɗan wasan mai shekara 24 na zaman aro a kungiyar ta Seria A tun farkon watan Janairu. (Calciomercato, via Sun)
West Ham da Aston Villa na cikin kungiyoyin da ke rububin saye ɗan wasan Colombia mai buga tsakiya James Rodriguez, ɗan shekara 30, daga Al Rayyan ta Qatar. (Fichajes – in Spanish)
Ɗan wasanGalatasaray da Denmark Victor Nelsson, ɗan shekara 23, ana alakanta shi da kokarin komawa Aston Villa. (Tum Spor – in Turkish)
Aberdeen ta bai wa Leeds damar tattaunawa da ɗan wasanta mai shekara 18 Calvin Ramsay. (Football Insider)
KocinNorwich Dean Smith na son sayo ɗan wasan Aston Villa Cameron Archer. Matashin mai shekara 20 na zaman aro a Preston. (TeamTalk)
Masu busa wasa a Firimiyar Ingila Martin Atkinson da Jonathan Moss za su yi ritaya a karshen wannan kakar. (Telegraph)
-
News4 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News2 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News4 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
