Connect with us

News

EFCC ta gano gidajen Akanta Janar guda 17 a Landan, Abuja, Legas, Kano da Dubai

Published

on

Daga maryam bashir Musa 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta bankado gidajen Akanta Janar na tarayya, Ahmad Idrs, guda goma sha bakwai (17).

Najeriya Na Bukatar Shugabanni Masu Dan Tabin Hankali — Obasanjo

Advertisement

Punch ta ruwaito cewa wani jami’in EFCC wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace Idris ya mallaki gidaje a Kano, Lagos, Abuja, Dubai da London

Ya kara da cewa an gani Ahmad Idris ya yi amfani da wasu makusantarsa wajen sayen wadannan dukiyoyi.

Advertisement

Jami’n yace ga dukkan alamu, ya mallakai wadannan dukiyoyin ne yayinda yake Ofis amma bai ayyana cikin takardar hukumar ladabtar da ma’aikata ba kamar yadda doka ta tanada.

Yace “Kimanin gidaje 17 a Kano, Lagos, Abuja, Dubai da London aka bankado mallakinsa. A Abuja, wasu gidajen na manyan rukunin gidaje.”

Advertisement

A cikin makon nan ne dai, hukumar EFCC ta awon gaba da Ahmed Idris wanda take zargin da yin ruf da ciki akan wasu kudade da keangilolin bogi, wanda adadin su ya kai naira biliyan tamanin.

Tuni dai ministar kudi Zainab Shamsuna ta bayyana dakatar da Ahmed Idris daga kan muƙamin sa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending