Uncategorized
Likitoci takwas za,a fara shariar su bisa laifin kashe maradona
Daga kabiru basiru fulatan
Ma,aikatan lafiya takwas ne za,a fara shariar da su bisa laifin zarginsu da akeyi da kissan maradona
Maradona ya mutu a watan Nuwamban 2020 a gidansa dake Buenos Aires, sakamakon bugun zuciya yana da shekaru 60.
Kafin mutuwarsa ya yi jinya bayan an yi masa tiyata a farkon watan da ya rasu.
Sai dai yan kwanaki bayan mutuwarsa ne masu shigar da kara suka kaddamar da binciken likitoci da sauran ma’aikatan lafiyar da suka yi jinyarsa.
Kuma a bara ne suka bada rahoton cewa akwai sakaci da rashin kwarewa ga wasu daga cikin ma’aikatan lafiyar da suka yi jinyar tasa.
Idan aka kama su da laifi a mutuwar tsohon dan kwallon na Argentina, za su iya fuskantar daurin shekaru 25 a gidan yari, kamar yadda kundin tsarin Mulki ya tanada
-
Opinion6 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion6 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News5 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
