News
Ruwan Sama Da Kankara Ya Lalata Gonaki 300 A Katsina
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Amfanin gona sun lalace a gonaki akalla 300 sunnan rufin gidaje da dama sun lalace a sakamakon ruwan sama da kankara a Karamar Hukumar Kafur ta Jihar Katsina.
Shugaban Karamar Hukumar Kafur, Garba Kanya, ya ce an yi asarar miliyoyin Naira a kogani sama da 300 da ke daf da girbe shinkafa, masara, gero, shinkafa, waken suya, albasa da barkono, a yankin.
Mutum Miliyan 50 Na Cikin Kangin Bauta Da Auren Dole A Duniya —MDD
“Halin Da Muka Shiga Bayan Ambaliya a Garin Karnaya”
Wani mazaunin kauyen Gozaki, Malam Abdullahi Gozaki, ya ce ba su taba ganin irin ruwan sama da kankara haka ba.
Ya bayyana cewa a cikin ’yan mintoci ruwan da kankara ya lakata gonaki da rufin gidaje tare da farfasa gialsan motoci da dama.
Malam Abdullahi ya ce sauran unguwannin da aka samu hakan su ne Dutsen-Kura/Kanya da Gozaki Gidan Danwada da kuma Gidan Sabo.
Sauran su ne; Kabalawa, Unguwar Tsamiya, Dandabo, Unguwar Maigarma, Unguwar Wanzamai da kuma Unguwar Fulani.
Shugaban Karamar Hukumar Kafur, Garba Kanya, ya ce sun sanar da Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Katsina da Hukumar Raya Karkara da sauran hukumomin da suka dace kuma sun zo sun gudanar da aikin tantance irin asara da aka yi.
DAILY TRUST
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
