News
Ganduje ya zargi yan kwankwasiyya da farmakar jama’ar gari ranar Lahadi
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADEEN
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, tace tana Allah wadai ta farmakin da tawagar kwankwasiyya ta tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, suka kaiwa jama’ar gari a ranar Lahadin da ta gabata, yayin bude ofishin yakin neman zaɓen jam’iyyar NNPP da ke unguwar Sharada a jihar Kano.
Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai na jihar Kano, kuma mai magana da yawun takarar Gawuna/Garo, kwamared Muhammad Garba, ya bayyana cewa sunyi takaici da abinda ya faru, domin sunyi tsammanin za’ayi yakin neman zaɓe cikin kwanciyar hankali, amma sai suka lura da yadda magoya bayan NNPP suka dauki muggan makamai harda ƙwacen Waya, a cewarsa.
Kwamishinan ya kara da cewa, tuni gwamna Ganduje ya ja hankalin jami’an tsaro akan lamarin, domin su ne masu alhakin tabbatar da zaman lafiya, da kuma tabbatar da cewa kowacce jam’iyyar ta gudanar da yakin neman zaɓenta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
Nassara radio
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
