Connect with us

Sports

An Sallami Toni Kroos Daga Wasa Karon Farko A Tarihi

Published

on

Toni Kroos lokacin da aka daga masa jan kati

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Hazikin dan wasan tsakiya na Real Madrid, Toni Kroos ya karbi katin sallama na farko a tarihin sana’arsa ta tamaula.

Kroos ya karbi jan katin yayin da Real Madrid ta raba maki da Girona, bayan da suka tashi 1-1 a wasan mako na 12 a gasar La Liga da suka fafata a Santiago Bernabeu ranar Lahadi.

Advertisement

NDLEA ta kama Wani basaraken gargajiya da laifin safayar miyagun kwayoyi

Tarihi ne wanda dan wasan ya kafa tsawon shekaru 15 da ya shafe a fagen sana’ar tamaula, inda a karshe ya karbi katin gargadi na biyu ana daf da tashi daga wasan.

Advertisement

Saura minti 20 a tashi daga wasan Real ta ci kwallo ta hannu Vinicius Junior.

To sai dai Girona ta farke ta hannun Cristhian Stuani a bugun fenariti, saura minti 10 lokaci ya cika.

Advertisement

Hakan ce Real ta karasa fafatawar da ’yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Toni Kroos jan kati daf da za a tashi daga wasan.

Karo na biyu da Real ta tashi 1-1 a gasar La Liga ta bana, bayan wanda ta yi a gida da Osasuna ranar 2 ga watan Oktoba a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Advertisement

Da wannan sakamakon Real Madrid ta koma ta daya a kan teburin La Liga da maki 32 da tazarar maki daya tsakaninta da Barcelona ta biyu.

Ranar Laraba 2 ga watan Nuwamba, Real Madrid za ta karbi bakuncin Celtic a wasan karshe a cikin rukuni a Champions League.

Advertisement

Kafin wannan karawar kungiyoyin sun yi wasa shida a tsakaninsu, inda Real Madrid ta yi nasara a hudu, Girona ta ci wasa biyu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending