Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Kashe ’Yan Kasuwa 4 A Katsina

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

Akalla ’yan kasuwa hudu ne ’yan bindiga suka hallaka har lahira a kauyen Zandam da ke Karamar Hukumar Jibiya ta Jihar Katsina.

Advertisement

 

Shugaban Karamar Hukumar Jibiya, Bashir Sabiu Maitan, ya shaida wa manema labarai cewa maharan sun kashe ’yan kasuwar ne a kan hanyarsu ta zuwa Kasuwar Jibiya da ke ci mako-mako a ranar Lahadi.kamr yanda jaridar aminiya ta rawaito

Advertisement

An kama sojojin Chadi da dama bisa kitsa juyin mulki

 

Wata majiya a kauyen Zandam, da ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa harin daukar fansa ne saboda, “Jiya (Asabar) wasu ’yan banga sun kashe wani Bafulatani, shi ne yau maharan suka kawo hari suka kashe mutum hudu a hanyar Kasuwar Jibiya.

Advertisement

 

“Mutum biyar suka harba, amma take hudu suka mutu, na biyar din, Malam Ibrahim Julius, yana asibiti yana jinya.”

Advertisement

 

 

Advertisement

Ko da aka tuntubi kakakin ’yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce wanda ya ji raunin yana kwance a Babban Asibitin Katsina.

 

Advertisement

Karamar Hukumar Jibiya na daga cikin yankunan da ke fama da hare-haren ’yan bindiga, lamarin da ya sanya gwamnatin jihar a baya-bayan nan ta bayar da umarnin rufe titin da ya tashi da Jibiya zuwa Zurmi a Jihar Zamfara.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending