Connect with us

News

’Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Mata 4 A Zamfara

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Yan bindiga sun kai hari kan dalibai mata na Kwalejin Lafiya ta Tsafe da ke Jihar Zamfara inda suka kwashe guda 4 bayan halartar wani bikin aure.

 

Advertisement

Bayanai daga yankin sun ce ‘yan ta’addar sun kama wadannan dalibai ne lokacin da suke komawa Kauran-Namoda daga Birnin Magaji.

 

Advertisement

Wata jami’a a Nijeriya ta hana ɗalibai amfani da wayoyin zamani

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne bayan tare motocin da ke dauke da wadanda abin rutsa da su, inda suka kwashi matafiya 18, cikinsu har da daliban mata 4 da wasu ’yan mata 3 da kuma wani mutum guda.

 

Advertisement

Tuni hukumomin Kwalejin Kula da Lafiyar ta hannun shugabansu Yusuf Maradun ya tabbatar da aukuwar lamarin wanda ya ce ba’a cikin makarantar aka kwashi daliban ba.

 

Advertisement

 

Maradun ya ce lokacin da aka sace wadannan daliban makarantar na hutun karshen shekara.

Advertisement

 

Wani dan uwan daya daga cikin daliban ya ce ‘yan ta’addar sun bukaci fansar Naira miliyan 20 kafin sakin diyarsu.

Advertisement

 

Jihar Zamfara na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro musamman hare- hare da kuma garkuwa da jama’a domin karbar kudin fansa.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending