Connect with us

News

2023: Kar ku bari shaidan ya rude ku a yi rigima lokacin zaɓe, Sheikh Nazifi

Published

on

 

 

Advertisement

Shahararren malamin addinin Musulunci a Kano, Sheikh Dakta Muhammad Nazifi Inuwa, ya ce yin rigima, har ta kai ga an yi kashe-kashe a lokacin zaɓe, babban laifi ne da ka iya janyo fushin Allah.

 

Advertisement

Sheikh Inuwa ya yi wannan gargaɗi ne a yau Litinin, yayin da ya ke gudanar da karatun littafin Riyadul Salihin, a masallacin Marigayi Abubakar Hussein da ke unguwar Fagge a jihar Kano.

Kotu ta umarci Ganduje da ya dawo da Muhuyi

A cewar malamin, kamata ya yi al’umma su fita su yi zaɓe, su kuma yi shi da kyakkyawar niyya, inda ya ƙara da cewa “sai kuma su raka da addu’a.”

Advertisement

 

Dakta Inuwa ya yi bayanin cewa idan mutane su ka kaɗa kuri’a, to su sun sauke nauyin su, sai kuma su jira hukuncin Ubangiji, wanda dama tuni Ya riga Ya san wanda zai lashe zaɓen.

Advertisement

 

Ya yi kira da cewa kada al’umma su bari a tunzura su har su ɗauki makamai su na saran juna har ya kai ga kisan kai, in da ya ce “wallahi duk wanda ya kashe wani, da wanda yai kisan, da wanda ya sa aka yi kisan, duk laifin su ɗaya kuma sai sun yi bayani a gaban Ubangiji a ranar alƙiyama.

Advertisement

 

“Idan ka yi zaɓe, to kai ka gama naka aikin; sai ka koma gida ka yi addu’a ka kuma sanya kyakkyawar niyya. Duk sakamakon zaɓen da ya fito, ko yai maka ko bai maka ba, to sai ka yi fatan alheri ka rungumi ƙaddara.

Advertisement

 

“Ina wa al’umma nasiha da kar su bari a zuga su suyi rigimar siyasa. Dan Allah dan Annabi a saka tsoron Allah a zuci a yi zaɓe lami lafiya,” in ji Shehin Malamin.

Advertisement

 

Ya kuma shawarci al’umma da su fito su yi zaɓe sannan su yi wa ƙasa Nijeriya addu’ar fatan alheri.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending