Wata kotu a Amurka ta yanke wa wani matashi farar fata hukuncin ɗaurin rai da rai ,ba tare da afuwa ba game da kisan baƙar fata 10 a wani babban kanti a Buffalo da ke jihar New York a watan Mayun bara.
Alƙalin kotun mai sharia Susan Eagan ta ce an yanke masa hukuncin da ake yanke wa manya duk da cewa shi matashi ne
Ta ce idan aka dubi yadda aka shirya bincike tare da aiwatar da wannan aika aikar ta nuna ƙiyayya, idan aka yanke ma ka hukunci a matsayin matashi toh wannan tamakar rashin adalci ne
Sai dai ‘yan uwan mutanen da ya kashe, da suka fusata sun far wa matashin mai suna Payton Gendon inda ɗaya daga cikinsu ya yi ƙoƙarin kai masa naushi.
Masu bincike sun gano cewa ya yi bincike ta intanet a kan adadin bakar fatar da ke zaune a unguwar da ya kai harin
