Connect with us

News

Buhari So Ya Ke APC Ta Fadi Zabe – inji Ganduje

Published

on

 

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kin bin umarnin kotun koli na ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudi.

Advertisement

Wannan na dauke ne cikin wani faifan murya, wanda aka jiyo Ganduje yana cewa, “Ya kamata shugaba Buhari ya tuna cewa sau da dama yana kokarin tsayawa takarar shugaban kasa amma bai samu nasara ba, amma yanzu yana so jam’iyyar ta rushe, baya ga tsarin dimokuradiyyar da ya ba shi damar shiga ofis”.

 

Advertisement

NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar watan Nuwamban 2022

Ya ce, “Ya kamata shugaban kasa ya tuna cewa wannan tsari ne na dimokuradiyya da ke bai wa jama’a damar sauraren shawarwari da kuma bin shawarwarin.

“Ina mamakin dalilin da ya sa shugaban kasa kayar da jam’iyyar da ta taimaka masa ya ci zabe, me muka yi masa”.

Advertisement

“Wannan siyasar canjin kudin, me yasa shugaban kasa bai kawo ta shekaru bakwai da rabi da suka wuce ba ko kuma bayan zabe ba, amma yanzu dole ne a tilasta wa mutum ya yi tunanin cewa akwai wata manufa a cikin wannan shirin.”

Ganduje, wanda ya yi wa Gwamnan CBN, Goodwin Emefiele wankin babban bargo, ya ce, “Gwamnan CBN bai san komai ba; game da wannan tsarin”.

Advertisement

Gwamnan ya damu matuka, inda ya ce Bankin Duniya da IMF da sauran Cibiyoyin Kudi sun shawarci Shugaban kasa da ya yi tunani kan wannan tsari amma ya yi kunnen uwar shegu da su.

A baya dai akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin Ganduje da shugaba Buhari, sai dai wadannan kalaman na nuni da cewa, ɓaraka ta riga ta kunno kai.

Advertisement

Tuni dai wasu daga cikin hadiman bangarorin guda biyu suka fara maida wa juna martani masu zafi a shafukan sada zumunta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending