Connect with us

News

Ɗage zaɓen gwamnoni ka iya shafar aikin ƙidayar 2023 – NPC

Published

on

Shugaban hukumar Kidayar jama’a ta Najeriya Nasir Isa Kwarra ya ce ɗage zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jihohi da ka yi a ƙasar ka iya shafar aikin ƙidayar jama’ar da aka shirya gudanarwa cikin watan Maris

Mista Nasir ya yi wannan iƙiƙari ne a lokacin da yake ganawa da wakilan asusun ƙidayar jama’a na Majalisar Dinkin Duniya a Abuja babban birnin ƙasar.

Advertisement

Mutum 2 Sun Yi Wa wata yarinya kurma mai shekara 15 fyade  A Nasarawa

Hukumar zaɓen Najeriya dai ta ɗage zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jihohi da aka shirya gudanarwa ranar 11 ga watan Maris zuwa ranar 18 ga watan Maris.

shugaban hukumar ƙidayar ya shaida wa manema labarai cewa duk da kawo yanzu ba a saka tartibiyar ranar fara aikin ba, zai tuntuɓi shugaban ƙasar Muhammadu Buhari domin saka ranar da za a fara gudanar da wannan aiki.

Advertisement

A nata ɓangaren wakiliyar asusun Majalisar Dinkin Duniya kan ƙidayar jama’a Ms Ulla Mueller, ta alƙawarta bayar da tallafin asusun domin tabbatar da gudanar da aikin kamar yadda aka tsara.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending