Uncategorized
NNPP ta bukaci a soke zaben gwamnan Borno
Jam’iyyar NNPP ta bukaci Hukumar INEC ta soke zaben Gwamnan Jihar Borno na ranar Asabar, ta gudanar da sabo.
NNPP reshen Jihar Borno ta yi kiran ne saboda rashin sanya sunanta da na dan takararta, Umar Alkali Nasko, a kan takardar kada kuri’a a zaben.
Shugaban NNPP a jihar, Barista Mohammed Mustapha, ya ce babu yadda za a yi su gama bata lokaci wajen yin yakin neman zabe, su gama kashe kudi, amma hukumar ta ki sanya sunan a jam’iyyar ko na dan takarar a takardar kada kuri’a.
Don haka ya ce za su dauki matakin ahari’a domin tabbatar da ganin hukumar ta soke zaben.
Amma a nasa bangaren, kakakin INEC a jihar, Abba Liberty, ya ce hukumar ba ta san da zaman dan takarar gwamnan NNPP a jihar ba, saboda ya yi lattin dawo da takardar tsayawarsa takara. Kamar yanda aminiya ta rawaito
