News
Ganduje ya na’da Farfesa Attahiru Jega A matsayin Shugaban Majalisar Gudanarwar Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi.
Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zamanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega a matsayin shugaban zartarwa Shugaban Majalisar Gudanarwar Sa’adatu Rimi dake Kano.
Hakan na cikin wata sanarwa ce da Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano kwamared Muhammad Garba ya fitar.
Kotu a Jigawa ta yanke hukunci kisa ta hanyar rataya kan wasu mutane 3
Sanarwa ce gwamna Ganduje ya kuma amince da naɗin Oba Dakta Sanata Moshood Olalekan Ishola Balogun na Aliiwo a matsayin babban uba kuma shugaban kwamitin gudanarwar Jami’ar ta Sa’adatu Rimi.
A cewar Muhammed Garba sauran mambobin kwamitin gudanarwar Jami’ar sun haɗa da: Dakta Muhammad Adamu Kwankwaso, Hajiya Zulaiha UM Ahmed, Dakta Ibrahim Yakubu Wunti, Dakta Halima Muhammad da kuma Alhaji Sabi’u Bako.
A baya-bayan nan ne dai hukumar kula da jami’o’i ta Nigeria (NUC), ta amince da ɗaga likkafar kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi zuwa Jami’a.
