Connect with us

News

Ana Fargabar Mutane Da Dama Sun Mutu a Kano Sakamakon Shan Shayin Zaƙami a Wurin Biki

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Ana fargabar samari da dama sun mutu wasu kuma na kwance magashiyyan a asibitin sakamakon shan shayin da ake zargin an dafa shi da ganyen zaƙami a wurin wani biki a unguwar Sheka da ke birnin Kano.

Advertisement

Zaƙami dai na dauke da sinadarin da ke kusan dauke hankalin mai sha kacokam.

 

Advertisement

Majalisar Sakkwato Ta Kafa Dokar Hana Tsadar Aure

Shaidun gani da ido sun ce akalla mutane 50 abin ya shafa.

Daya daga cikin wadanda suka shaida lamarin mai suna Sunusi Yahaya, wanda yaya ne ga amarya, ya ce bayan dafa shayin da zaƙami, akwai muggan kwayoyi masu bugarwa ma da samarin suka zuba a cikin shayin kuma suka dafa da su.

Advertisement

Yace yanzu abin ya zama ruwan dare ga matasa a yankin, a duk lokacin da suke biki, sai su dafa shayin da suke zuba masa muggan kwayoyi a ciki, su fake da shan shayi domin su yi shaye shaye.

Sunusi ya ce saboda ƙarfin kwayoyin da yaran suke sakawa a shayin ta kai ta kawo wasu ma basa iya sha, wasu kuwa a hakan suke shanyewa wai ala dole sai sun bugar da kan su.

Advertisement

Yace tun a ranar bikin, nan take mutum biyu suka mutu bayan sun sha shayin.

Wani wanda ya shaida lamarin ya bayyana cewa, izuwa ranar Talata, mutane 7 ne suka mutu, kuma da dama suna kwance a asibiti.

Advertisement

Yace wasu ma ba yan unguwar bane, kawai sun zo wucewa ne suka ga ana shan shayin suka tsaya suka sha, daga nan kuma mai afkuwa ta afku.

Wasu kuma ba ma gayyatar su aka yi ba, takanas suka zo yin shaye shayen su.

Advertisement

Rahotanni sun ce angon ma ya ranta a na kare tare da wasu abokansa tun da abin ya faru.

Yunkurin jin ta bakin kakakin rundunar yan sanda na jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending