Connect with us

News

Farashin Sadaki Yayi Tashin Gwauron-Zabi a Najeriya

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

A ranar Juma’a, 12 ga watan Dhul Hijjah Hijira 1444, wacce ta yi daidai da 30 ga watan Yunin 2023, fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi ta fitar da sanarwar nisabin Zakkah, Sadaki da Diyyar rai.

Advertisement

Wannan na zuwa ne kwanaki biyu kacal da gudanar da idin babbar Sallah da aka gudanar a ranar Laraba 10 ga watan Dhul Hijjah na wannan shekarar.

A cikin sanarwar da sarkin Musulmin ya fitar, wacce hukumar kula da ganin jinjirin wata ta yada a shafinta na Facebook, an bayyana adadin kudade ga kowane bangare.

Advertisement

A cewar sanarwar, yanzu nisabin Zakkah ya koma Miliyan 3 da dubu 918 da Naira 800, wanda aka kwatanta da darajar farashin kwal a duniya.

A bangaren haddin sata da kuma sadaki na auren mace, dole sai ya kai akalla N48,985 kafin ya cika ka’idar shari’a.

Advertisement

Abin da hakan ke nufi shine, ana yanke hannun barawo ne idan a shari’ance idan ya saci dukiyar da ta kai aalla N48,985.

Hakazalika, a shari’a dole mai neman aure ya ba da sadakin da bai yi kasa da N48,985 ba don cikar ka’idar daurin aure.

Advertisement

A bangaren Diyyar rai, ana daurawa wanda ya yi kisa biyan Diyya ne a kan kudi Miliyan 195 da dubu 940. duba da darajar kudade da ake dasu a yanzu.

Wadannan na kadan daga cikin hanyoyin da addinin Islama ya tanada don yiwa kowa adalci a fannin gudanar da rayuwar yau da kullum.

Advertisement

A shekarun da suka gabata, majalisar koli ta addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta bayyana nisabin karancin sadaki a kasar nan.

Sheikh Khamis Al-Misriy, limamin masallacin Abu Ubaidah Bn Jarrah dake bye-pass jihar Kaduna, yayi bayanin yadda abubuwan suke

Advertisement

Kamar yadda malamin ya sanar, nisabi dai shine wani ma’auni da ake gwadawa domin a gane darajar kudi da inda ya kai.

A musulunce kuwa ana kiran shi da kaso daya bisa hudu na dinari daya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending