Connect with us

News

Kwalejin Ilimi ta tarayya dake Bichi a Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar dalibinta.

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Kwalejin Ilimi ta tarayya dake Bichi a Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar Japheth Solomon, dalibin aji 2 na sashen koyar da Ilimin kasuwanci.

Advertisement

Cikin wata sanarwa da Fatima Hassan Ahmad Daraktar yada labarai da hulda da Jama’a ta kwalejin ta fitar, ta ce da yammacin ranar Litinin 17 ga Yuli, 2023 kwalejin ta samu labarin wata takaddama da ta barke tsakanin wani dalibi a wajen makarantar mai suna Japheth Solomon da wani dan kauyen Buden waje dake makwaftaka da makarantar.

Gwamnan Abba Ya Nada Sabbin Mukamai 14 A Hukumomi Da Ma’aikatu jahar.

Rahotanni sunce an yanku Japheth a wuyan hannunsa inda bokan karatunsa ne suka garzaya da shi Babban Asibitin Bichi sai dai ya zubar da jini da yawa kuma cikin duba lafiyarsa rai ya yi halinsa.

Advertisement

 

Fatima Hassan ta ce hukumar gudanarwar kwalejin ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki a safiyar ranar talata 18 ga watan Yuli, 2023, inda ta gabatar da jawabi ga daukacin daliban Kwalejin tare da ayyana makokin kwana biyu.

Advertisement

 

Shugaban kwalejin Dr Bashir Sabo Abubakar ya yi kira ga daukacin daliban da su yi taka tsantsan wajen kare lafiyarsu.

Advertisement

 

Kwalejin tace tana aiki tare da ‘yan sanda da sauran wadanda abun ya shafa don tabbatar da adalci akan al’amarin.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending