Connect with us

News

Motoci Makare Da Kaya Sun Makale A Kan Iyakar Najeriya Da Jamhuriyar Nijar

Published

on

Wasu Motoci Kenan Akan Iyaka

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Motocin da ke cike da kaya da ke shiga Nijar a halin yanzu sun makale a garin Jibia da ke kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

Hakan na zuwa ne bayan da gwamnatin tarayya ta rufe dukkan iyakokin kasa da jamhuriyar Nijar bayan hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum da sojoji suka yi.

Advertisement

Gwamnan jihar Zamfara ya jaddada aniyar gwamnatinsa na magance matsalolin tsaro da ke addabar jihar 

Wani dan jarida da ke kan iyaka a ranar Juma’a ya kirga motoci sama da 30 da aka jera a bangarorin biyu na babbar hanyar daga jamhuriyar Nijar

Premium Times ta ruwaito cewa kuma Akwai manyan motoci da aka jera a kan titin daga bangaren Najeriya, da fatan a ba su izinin shiga jamhuriyar Nijar
Mukaddashin kwanturolan hukumar kwastam, Bashir Adeniyi, ya ce ba za a bari motocin su shiga ko fita ba a yanzu
Muna da manyan motocin da ke zuwa daga Najeriya wadanda ba za su iya zuwa wani bangaren (Jamhuriyar Nijar) ba
Da yawa daga cikinsu suna cikin Katsina idan za ku iya kunna kyamararku, za ku ga abin da muke da shi ma a can inji wani direba da ya Tattauna da yan jarida
Akwai direbobi da mataimaka da dama zaune a karkashin wata bishiya da ke daf da inda aka ajiye motocin

Advertisement

Muna cikin wani mawuyacin hali. Na zo nan ne kafin a rufe iyakar a hukumance amma kafin in samu izini, sai (hukumomin kan iyaka) suka ce sun samu sigina daga Abuja na rufe dukkan iyakokin inji wani direban da ya makale a bakin iyakar

Ya ce ya kashe duk kudin cin abincinsa saboda ranar Juma’a ce kwana na hudu da yayi a kan iyaka

Advertisement

Wani direban da ya makale, ya ce zai yaba idan kasashen biyu suka kawo karshen lamarin

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending